in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya jaddada bukatar magance cin zarafin mata
2017-11-23 10:54:10 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya nanata muhimmancin kawar da matsalar cin zarafin mata.

Guterres ya ce, kowace mace da kuma kowace yarinya na da 'yancin yin rayuwa cikin 'yanci ba tare da muzgunawa ba. Amma a cewarsa har yanzu ana fama da yawaitar abubawa na keta hakkin dan adam a cikin kowace al'umma. Ya ce yawanci wannan matsalar tafi shafar mutanen da ba su da galihu ne a cikin al'umma musamman wadanda aka mayar da su saniyar ware.

Jami'in MDDr yayi wannan tsokaci ne a lokacin wani gangami na tunawa da ranar yaki da cin zarafin mata na kasa da kasa wanda aka ware 25 ga watan Nuwambar kowace shekara.

Ya kara da cewa a duk fadin duniya, a cikin mata 3, mace guda ta taba fuskantar wani nau'in cin zarafi a rayuwarta, an yiwa mata miliyan 750 aure kafin su cika shekaru 18 da haihuwa, kuma sama da mata miliyan 250 ne aka yi musu kaciya.

An samu karuwar kaddamar da hare hare kan mata masu fafutukar kare 'yancin matan, wadanda suke gwagwarmayar kwatar 'yancin mata da tauye musu hakki a fannonin siyasa, da cigabansu a fannonin zamantakewa, tattalin arziki, da al'adu, da kuma cin zarafin mata ta hanyar fyade a lokutan da ake fama da tashe tahen hankula, inda jami'in na MDD yace babu wasu alamu dake nuna ana samun raguwar matsalaolin cin zarafin mata a duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China