Bikin baje kolin zai gudana ne tsakanin jiya Talata zuwa Juma'ar karshen makon nan, ya kuma samu halartar wakilai daga masana'antu na kasa da kasa kimanin 230 daga kasashe 25, kamar dai yadda mashiryan sa suka bayyana.
Rahotanni daga ma'aikatar cinikayyar kasar Habasha na cewa, kasar ta samu kudaden shiga da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 90, daga hada hadar hajojin masaku a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017. Wadannan kudade dai sun fito ne daga ribar masana'antun kasar na samar da hajoji, musamman ma irin kamfanonin da ke sabon yankin bunkasa masana'antu na Hawassa na 'yan kasuwa Sinawa.