in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen sama na kasar Habasha yana cigaba da jan hakilin Sinawa masu yawon bude ido
2017-10-15 13:57:32 cri
Kamfanin sufurin jiragen sama na Ethiopian Airlines (ET), yana kokarin jan hakilin Sinawa masu yawon bude ido.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Asabar, babban jami'in gudanarwa na kamfanin na ET, Tewolde GebreMariam, ya bayyana cewa tun lokacin da jirgin ya fara mu'amalarsa da kasar Sin a shekarar 1973, ya kasance a matsayin wata babbar shaida dake tabbatar da sauya fasalin tattalin arziki ga babbar kasar ta nahiyar Asiya.

A halin yanzu, kasar ita ce kasuwa daya tilo mafi girma na kamfanin jiragen saman na Ethiopian Airlines mai wuraren sauka da tashi kimanin 5, inda jiragen ke zirga zirga sau 31 cikin kowane mako, ya kara da cewa, jirgin na ET shine babban kamfani mafi yawan zirga zirga tsakanin kasar Sin da Afrika, kana ya dauki Sinawa ma'aikatan jirgi masu yawan gaske wadanda ke kula da harkokin zirga-zirga zuwa kasar Sin.

Gebremariam yace, ana fatan dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika da kuma tsakanin Sin da Habasha zata kara bunkasuwa cikin sauri, da kuma samun karuwar cinikayya, zuba jari, da cigaba fannin yawan bude ido, kana yace suna fata mu'amalar dake tsakanin kamfanin na ET da kasar Sin zata cigaba da samun tagomashi a nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China