in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yi gargadin barkewar yunwa a Yemen
2017-11-09 12:37:01 cri

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai da agajin gaggawa Mark Lowcock ya yi gargadin cewa, muddin ba a cire takunkumin zirga-zirga ta sama da ruwa da ta kasa da dakarun kawancen da Saudiya ke jagoanta yake sanyawa ba, to za a samu barkewar yunwa da duniya ba ta taba ganin irinta ba a kasar Yemen.

Mark Lowcock wanda ya bayyana hakan yayin da yake yiwa kwamitin sulhu na MDD bayani game da yanayin jin kai da ake ciki a kasar ta Yemen, ya ce, wannan matsala za ta shafi miliyoyin jama'a, a don haka muddin ana son a magance wannan matsala, wajibi ne a aiwatar da wasu matakai guda biyar da ya gabatar. Na farko a dawo da zirga-zirgar jiragen sama na MDD da kawayenta zuwa manyan biranen Sanaa da Aden na kasar Yemen, tare ba da tabbacin cewa, ba za a dakatar da zirga-zirgar jiragen ba, sannan ba za a hana jiragen hukumar tsara shirin samar da abinci ta duniya wadanda ke gabar ruwan Aden gudanar da ayyukansu ba.

Tawagar kasar Sweden da ke MDD ce ta bukaci babban jami'in na MDD ya yi wa kwamitin sulhun MDDr bayani game da yanayin da ake ciki a kasar ta Yemen.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China