An bada tabbacin ne yayin wani taron ministocin harkokin waje da shugabannin dakarun kasashen da ke cikin kawancen, wadanda ke yaki a Yemen sama da shekaru 2 da suka gabata.
Taron ya tabbatar da cewa, an kaddamar da ayyukan sojin ne bisa bukatar Gwamnatin Yeman da aka zaba ta yaki da 'yan tawaye.
Mahalarta taron sun zargi Iran da mara baya ga 'yan tawayen wajen gudanar da muggan ayyukansu kan fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba tare da tada zaune tsaye a Yemen.
Sun kuma amince su ci gaba da samar da agajin jin kai domin tallafawa al'ummar kasar rage radadin yanayin da suke ciki.
Babu wasu alamomi dake nuna ranar da yakin da aka fara a watan Maris na 2015 zai kawo karshe, musammam bayan ganin an gaza tattaunawa tsakanin bangarorin siyasar kasar. (Fa'iza Mustapha)