Cibiyar MGI ta kasa da kasa dake nazari a fannin fasahohin zamani, ta fidda wani rahoto wanda ya nuna yadda kasar Sin ta shige sahun gaba a fannin raya fasahohin zamani, matakin da ke samar da karin damammaki na bunkasa ci gaban tattalin arzikin ta a sassa daban daban.
Rahoton ya ce inganta fannin fasahar zamani, na sauya hanyoyin samar da riba daga kirkire kirkire, yana kuma baiwa Sin din damar takara a fannonin tattalin arziki, ta yadda hakan ka iya ingiza sabbin kafofi na bunkasuwa.
Kaza lika rahoton ya nuna cewa, darajar hada hadar cinikayya ta kafofin na'urori masu kwakwalwa dake wakana a kasar Sin, ya haura yawan wanda ke wakana a kasashen Faransa, da Jamus, da Japan, da Birtaniya da ma Amurka baki daya.
A shekarar 2016 da ta gabata, adadin biyan kudade ta hanyoyin tafi da gidan ka da aka gudanar a Sin, ya kai dalar Amurka biliyan 790, adadin da ya kai linki 11 na wanda aka gudanar a Amurka a shekarar.
A daya hannu kuma, kasar ta Sin na cikin kasashe 3 dake sahun gaba a fannin zuba jari fannonin fasahar zamani, bangaren na'urorin amfanin gida, da na wasanni, da na ababen hawa, da na dab'i salon 3D, da na butun butumi, da na jirage marasa matuka da masu sarrafa kan su.
Rahoton ya kara da cewa, daya bisa 3 na kamfanoni rukunin unicorn 262, wadanda ke hannun sassan da ba na gwamnati ba, masu jarin sama da dalar Amurka biliyan daya na kasar Sin ne. Kamfanonin da kuma su ke rike da kaso 43 bisa dari, na daukacin jarin rukunin wadannan kamfanoni.(Saminu Alhassan)