in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana sahun gaba a duniya na rijistar lambar mallakar fasaha
2017-03-23 10:06:41 cri

Hukumar kula da harkokin ciniki da masana'antu ta kasar Sin SAIC, ta sanar a jiya Laraba cewa, kasar Sin ta shigar da bukatar yin rajistar lambar shaidar mallakar fasaha da yawansu ya kai miliyan 3 da dubu 690 a shekarar 2016, lamarin da ya zarta kashi 28.4 idan aka kwatanta da na shekarar 2015.

Sahihan lambobin mallakar fasaha da aka yiwa rijista a kasar Sin sun kai miliyan 12 da dubu 400 ya zuwa karshen shekarar 2016.

Kasar Sin ta kasance a kan gaba a duniya na yin rajistar cikin shekaru 15 da suka gabata.

Majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ta kaddamar da hakikanan ayyuka a fannin raya mallakar fasaha yayin da take aiwatar da shirinta na raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13 tsakanin shekarun 2016-2020.

Za a gudanar da bikin lambar shaidar mallakar fasaha na kasar Sin ne a watan Satumba mai zuwa, kuma bikin zai mayar da hankali ne kan irin rawar da lambar mallakar fasaha ke takawa gami da shirin nan na ziri daya da hanya daya, kamar yadda Wang Peizhang, shugaban kungiyar lambar shaidar mallakar fasaha ta kasar Sin ya tabbatar da hakan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China