A jiya Laraba ne aka bude taron baje kolin kayayyakin kere kere masu amfani da manyan fasahohi na zamani karo na 18, a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Taron na bana dai zai mai da hankali ne ga zakulo hanyoyin bunkasa sabbin masana'antu, da fadada hanyoyin zamanantar da masana'antu, ta yadda za su rika amfani da manyan fasahohi na zamani.
A cewar magajin garin Shenzhen Xu Qin, bikin na wannan karo ya samu halartar masu baje fasahohi sama da 3,000 daga kasashe 37, inda kuma ake sa ran baje hajoji da yawan su ya kai 10,000. Kaza lika yawan baki mahalarta baje kolin ya kai sama da mutane 500,000. (Saminu)