Ministan yada labaran kasar mai kula da yankin kudancin jahar Liech Peter Makouth Malual ya bayyana cewa, fadan ya barke ne a farkon wannan mako tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawayen (SPLA-IO), wadanda ke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, kuma an cigaba da gwabza fadan har zuwa ranar Laraba.
Malual ya ce, akalla 'yan tawaye 20 da kuma sojojin gwamnati 5 ne aka kashe a lokacin tashin hankalin. Sai dai ministan ya dora alhakin tayar da rikicin kan 'yan tawayen.(Ahmad Fagam)