in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan zai ziyarci Uganda domin karfafa dangantaka
2017-11-13 09:30:32 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa kasar Uganda tun daga yau Litinin da nufin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta rawaito.

Ziyarar shugaba al-Bashir ta kasance amsa goron gayyata ne da shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya aike masa.

Rahotani sun bayyana cewa dangantaka tsakanin Sudan da Uganda ta yi matukar kyautatuwa a 'yan shekarun nan bayan da aka samu tsamin dangantakar a tsakaninsu a shekarun baya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China