Rahotanni na cewa, Basaraken ba ya goyon bayan yunkurin gwamnatin kasar na kwance damarar dakarun da suke yankin Darfur. Bisa jagorancinsa, wata kungiya mai suna "kwamitin juyin juya-hali da neman fadakarwa na kasar Sudan"(ARC) ta ki martaba umarnin da gwamnatin kasar ta bayar, inda dakarun kungiyar ke ci gaba da rike kananan makamai.
A nata bangaren, gwamnatin kasar Sudan ta himmatu wajen aiwatar da manufarta ta kwace dukkan makamai daga dakaru da kananan bindigogi dake hannun kabilu daban daban a yankin Darfur, ta yadda sojojin gwamnati za su samu damar kula da yanki ba tare da wata matsala ba.
Kafin haka, bayanai na cewa, a ranar Lahadi da ta gabata, wasu sojojin gwamnatin kasar Sudan sun yi taho-mu-gama da dakarun kungiyar ARC ta kasar Sudan masu adawa da gwamnati, a jihar arewacin Darfur ta kasar Sudan.(Bello Wang)