in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fararen hular Yemen sama da dubu 5 sun rasu sakamakon barkewar rikice-rikice
2017-09-06 10:14:51 cri
A jiya Talata, ofishin ma'aikatan musamman dake kula da harkokin kare hakkin dan Adam na MDD ya fidda wani rahoto, inda ya bayyana cewa, tun daga watan Maris na shekarar 2015, ya zuwa yanzu, fararen hula na kasar Yemen sama da dubu 5 sun rasa rayukansu, sakamakon rikice-rikice da suka rika aukuwa a kasar, kuma kimanin kashi daya bisa biyar na wadanda suka rasun yara ne kanana.

Cikin wannan rahoto din, an bayyana cewa, dukkan bangarori masu hannu a tashe tashen hankulan kasar Yemen, sun taba aikata al'amura masu nasaba da keta hakkin dan Adama masu tsanani. Kaza lika, hare-hare ta sama da rundunonin sojojin wasu kasashe suka rika kaddamarwa a wasu sassa na kasar cikin hadin gwiwa bisa jagorancin Saudiya, sun haddasa rasuwar fararen hula masu tarin yawa.

Ban da haka kuma, wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, sun shiga kasar tare da bunkasa cikin sauri, sakamakon yanayin tashe-tashen hankula da aka sha fama da su a kasar. Lamarin da ya haddasa karin barazana a kasa ta Yemen.

Bugu da kari, an ce, cikin jimillar adadin 'yan kasar miliyan 27, mutane kusan miliyan 19 na bukatar taimakon jin kai. A sa'i daya kuma, mutane miliyan 7.3 daga cikinsu suna fama da karancin abinci.

A watan Satumba na shekarar 2014, kungiyar dakaru ta al-Ḥuthiyyun ta mamaye birnin Sanna, fadar mulkin kasar Yemen, sa'an nan, ta ci gaba da mamaye yankunan dake kudancin kasar, lamarin da ya sa, shugaban kasan kasar Abdu Rabbih Mansour Hady, da mambobin majalisar ministocin kasar suka yi gudun hijira zuwa kasar Saudiya.

A watan Maris na shekarar 2015 kuma, wasu kasashe da suka hada da kasar Saudiya, suka fara daukar matakan soja kan kungiyar dakarun al-Ḥuthiyyun, a sa'i daya kuma, ana kokarin yin shawarwarin neman sulhu da bangarorin da rikicin kasar ta Yemen ya shafa, bisa shiga tsakanin MDD.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga cimma matsaya game da rikicin kasar ba tukuna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China