Guterres ya karanta wannan sanarwa ga 'yan jarida cewa, bai kamata ba tsarin bauta ya cigaba da kasancewa a duniya a halin yanzu, tilastawa mutane zama bayi yana daya daga cikin miyagun ayyukan keta hakkin dan Adam, watakila zai zama laifin kiyayya ga dan Adam. Ya jaddada cewa, ya kamata a warware batun bakin haure ta hanyar jin kai, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa wajen yaki da sayar da mutane.
Guterres ya kalubalanci hukumar da abin ya shafa da ta yi bincike kan batun ba tare da bata lokaci ba, kuma ta gurfanar da masu aikata laifin a gaban kotu. Ya bayyana cewa, ya riga ya bukaci hukumomin MDD su yi bincike kan batun.
Kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun bayar da labari a makon da ya gabata cewa, an sayar da bakin haure na Afirka da suka tsaya a wurare daban daban na kasar Libya a matsayin bayi. A ranar 19 ga wannan wata, gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar Libya ta sanar da yin bincike kan batun. (Zainab)