in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon kundin kungiyar Hamas ya nuna goyon baya ga kafa kasar Falasdinu bisa iyakokin da aka shata a shekarar 1967
2017-05-02 14:10:17 cri
Kungiyar Hamas ta gabatar da sabon kundinta, wanda a ciki ta ce ta amince da kafa kasar Falasdinu, bisa iyakokin da aka shata a shekarar 1967 a yammacin kogin Jordan da kuma zirin Gaza.

Shugaban kungiyar Khaled Meshaal ne ya sanar da sabon shirin, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Doha na Qatar.

Sabon kundin ya jadadda cewa, bai amince da Isra'ila ba, kuma Hamas za ta yaki wadanda suka mamaye yankin Falasdinu.

Sai dai, kungiyar ta ce tana girmama Yahudawa kuma ba ta da matsala da su ko sauran addinai.

Hamas ta ce har yanzu tana ganin daukar makamai a matsayin hanya daya tilo ta 'yanta iyakokin Falasdinu.

Sai dai, Meshaal ya kara da cewa a yanzu, kungiyar ba ta da wata alaka da kungiyar 'yan uwa muslmi wanda a baya ta kasance wani bangare nata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China