A jawabinsa yayin taron, mukadashin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya ce, batun Falesdinu batu ne mai muhimmanci a yankin Gabas ta tsakiya, shi ne kashin bayan tabbatar da zaman lafiyar yankin baki daya. A don haka, ya kamata a warware batun Falesdinu cikin yanayin adalci a dukkan fannoni, lamarin da zai dace da moriyar al'ummomin yankin, da kuma ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa wajen neman hanyar warware matsalolin yankin Gabas ta tsakiya, domin shimfida zaman lafiya a yankin, da ma ci gaban yankin baki daya. (Maryan)