in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji sun halaka mayakan Boko Haram a Najeriya
2017-11-08 09:19:28 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram da dama, yayin da suka yi yunkurin kai wani hari a garin Gulak na jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake karin haske kan lamarin, shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Mohammed, ya tabbatar da cewa, sojojin sun shafe sa'o'i da dama suna bata kashi da mayakan na Boko Haram a lokacin da suka yi kokarin shiga garin na Gulak a ranar Litinin. Sai dai bai bayyana adadin 'yan Boko Haram din da aka halaka ba.

Ya ce, wasu mata biyu masu shekaru 70 da kuma 30 sun samu raunin harsasai yayin da suke kokarin tsira da rayukansu.

A halin da ake ciki kuma, kansila mai wakiltar mazabar Gulak Mohammed Abubakar ya shaidawa manema labarai cewa, mazauna garin da suka gudu sakamakon wannan lamarin sun dawo gidajensu.

Ana dai zargin Boko Haram da halaka mutane sama da 20,000 baya ga wasu mutane miliyan 2.3 da suka bar muhallansu, tun bayan da kungiyar ta fara kaddamar da hare-hare a kasar a shekarar 2009.

A farkon wannan shekarar ce dai sojojin Najeriyar suka yi nasarar fatattakar mayakan kungiyar Boko Haram daga sansaninsu dake dajin Sambisa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China