in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da hallaka mayakan ta 3
2017-11-27 09:17:32 cri

Rundunar sojojin tarayyar Najeriya ta tabbatar da rasuwar mayakan ta 3, baya ga wasu 6 da suka jikkata, yayin wani artabu da suka yi da 'yan Boko Haram a garin Magumeri dake jihar Borno.

Kakakin rundunar Timothy Antigha ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, dakarun sojin Najeriyar sun kwashe sa'o'i kusan biyu suna dauki ba dadi da mayakan na Boko Haram da yammacin ranar Asabar, kafin su kai ga korar su daga garin.

Antigha ya ce, 'yan ta'addan sun yi yunkurin kwace garin ne wanda ke da nisan kusan kilomita 35 daga arewacin birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar ta Borno.

A baya ma dai mayakan na Boko Haram sun sha yunkurin kwace garin Magumeri, sai dai har yanzu hakar su ba ta cimma ruwa ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China