in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun gwamnatin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 14 yayin wata arangama
2017-11-29 10:01:50 cri

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da hallaka mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram 14 a yayin wani samame da sojojin kasar suka kaddamar don kakkabe maboyar 'yan ta'addan a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya Sani Usman, ya bayyana cewa, kimanin fararen hula 30 ne suka ceto daga hannun mayakan a lokacin samamen a yankin Bama dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar a ranar Asabar din da ta gabata.

Usman ya ce, sun yi nasarar damke guda daga cikin mayakan na Boko Haram.

Dakarun Najeriyar sun samu nasarar lalata maboyar mayakan a kauyuka 8 dake yankin Bama.

A ranar Larabar makon jiya, sojojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram wadanda ba'a san adadinsu ba, kana sun lalata wani wuri da 'yan ta'addan ke hada boma bomai a lokacin da sojojin suka kaddamar da hare hare ta jiragen sama a jihar Borno.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China