Gidan rediyon Sham FM na kasar Syria ya ruwaito cewa, shingen binciken da aka kaiwa harin na zaune ne a tsakanin rijiyoyin hakar mai ta Jafra da ta Conico dake jihar Deir al-Zour, wanda ke karkashin sojojin demokuradiyya na Syria da mayakan Kurdawa ke jagoranta.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syria dake da mazauni a birnin London na Birtaniya, ta ce harin ya haddasa mutuwar mutane kimanin 50.
Wannan ne karo na biyu cikin wannan wata, da aka kai harin bom a cikin mota jihar Deir al-Zour. Ko a ranar 4 ga wata, an kai makamancin harin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 40. (Zainab)