in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ware yuan biliyan 124 don inganta rayuwar jama'arta
2017-12-01 10:20:47 cri

Hukumomin kasar Sin sun tabbatar da cewa kimanin yuan biliyan 124.4 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 18.8 ne kasar ta ware a kasafin kudinta domin amfani da su a matsayin kudaden tallafi don inganta rayuwar al'ummar kasar a shekara mai zuwa.

A cewar wasu bayanai da ma'aikatun kudi, da na kula da jin dadin jama'a, da ma'aikatar samar da gidaje da raya birane na kasar suka fitar, daga cikin jimilar kudaden, za'a kashe yuan biliyan 92.86 wajen tallafawa al'ummar sinawa dake fama da matsalolin karancin kudi.

Za kuma a yi amfani da yuan biliyan 10.79 wajen biyan kudaden jinya ga marasa lafiya wadanda suke cikin halin tsananin bukatar taimako kuma ba su da halin da za su iya biyan kudaden maganin, sannan za'a kashe yuan biliyan 18.59 wajen gyara gidajen da suka lalace a yankunan karkara da kuma yuan biliyan 2.1 wajen tallafawa nakasassu.

Gwamnatin kasar Sin tana baiwa shirin yaki da talauci fifiko musamman a 'yan shekarun nan. Gwamnatin ta sha alwashin tsame jama'arta daga cikin kangin fatara nan da shekarar 2020 a lokacin da kasar ke fatan cimma burinta na samar da al'umma mai matsakaiciyar watada.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China