in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon bayan yiwa ayyukan samar da zaman lafiya na MDD gyaran fuska
2017-09-21 19:14:28 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya nanata kudurin kasarsa na goyon bayan yiwa ayyukan samar da zaman lafiya na MDD gyaran fuska, ta yadda za su dace da yanayi da ka'idojojin MDD.

Mr Lu Kang wanda ya bayyana hakan yayin taron maname labarai, ya ce minsitan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi Karin haske game da matsayin kasar Sin yayin taron manyan jami'ai game da wannan batu.

Ya ce har kullum kasar Sin tana goyon baya kuma tana tare da shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

A jiya ne dai babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar da wasu shawarwari guda 4 game da yada za a yiwa ayyukan samar da zaman lafiya na majalisar gyaran fuska. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China