Wannan shiri na bai daya, zai kunshi bayanai game da adadin cibiyoyin kula da tsoffin da ake da su, da yadda ake aikin ba su hidima, da ingancin aikin, da tabbatar da ba su tsaro, da kuma adadin jami'an dake gudanar da ayyukan.
Ma'aikatar ta ce, ta fara shirin ba da horo game da yadda za'a gudanar da sabon tsarin, kuma za a shigar da bayanan farko na wannan shirin ne a ranar 10 ga watan Mayu.
Batun tsofafi a kasar Sin ya kasance wani muhimmin batu game da sha'anin yanayin zaman rayuwa. A halin da ake ciki, kasar na da adadin mutanen da shekarunsu suka zarta 60 kimanin miliyan 220, wato kashi 16.1 cikin 100 na yawan al'ummar kasar baki daya, kuma adadin na ci gaba da karuwa.
Hakan ya sa mahukuntan kasar ke ta hankoron lalibo hanyoyin da za'a inganta tsarin, da kuma magance manyan kalubalolin da ake fuskanta game da batun na tsoffi. (Ahmad Fagam)