Xi ya jaddada cewa, Sin na son hada kai da Amurka, domin karfafa mu'amala da hadin-gwiwa tsakaninsu, tare kuma da kara habaka alakokinsu.
Shi ma a nasa bangaren, Obama cewa ya yi, ci gaban da kasar Sin ta samu abin yabo ne ga duniya. Raya dangantaka tsakanin Sin da Amurka na dacewa da muradun al'ummar kasashen biyu, kuma shi kansa zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen kara samun fahimtar juna da inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu.(Murtala Zhang)