Shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin zai halarci bikin kaddamar da taron, tare da gabatar da jawabi.
A yayin taron manema labaru da aka shirya yau, mataimakin babban direktan hukumar dake lura da mu'amalar jam'iyyun siyasa na kasashen waje ta kwamitin kolin JKS Mr. Gou Yezhou, ya bayyana yadda ake share fagen taron, ya kuma amsa tambayoyin da manema labaru suka gabatar.
Mr. Gou ya ce, babban jigon taron shi ne "nauyin da ake dorawa jam'iyyun siyasa wajen bunkasa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama." Ya ce zuwa yanzu, yawan adadin jam'iyyun siyasa da suka fito daga kasashe fiye da 120, kuma suka yi rajistar halartar taron ya kai fiye da dari 2.
Mr. Gou ya tabbatar da cewa, yanzu haka ana share fagen taron kamar yadda ya kamata. Kaza lika ya amince da cewa, bisa kokarin jam'iyyun siyasa da za su halarci taron, ko shakka babu wannan taro zai bayar da muhimmiyar gudummawa game da yadda za a iya kara fahimtar juna, da cimma matsaya daya kan batutuwa iri iri, da kuma bunkasa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin jam'iyyun siyasa na kasashen duniya. Har ila yau an yi hasashen cewa, za a iya fitar da wata takarda game da sakamakon da za a samu a yayin taron. (Sanusi Chen)