in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi kira da a baiwa nakasassu karin kulawa
2017-11-30 13:52:39 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce nakasassu ko masu bukata ta musamman bangare ne na al'ummar duniya, don haka akwai bukatar baiwa bukatun su dukkanin kulawa da ta dace.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana hakan ne, cikin sakon sa na taya murnar bude taron wakilan gwamnatoci na yankin Asiya da Fasifik, game da auna halin da masu bukata ta musamman ke ciki.

Taron wanda aka bude a ranar Litinin a nan birnin Beijing, na mai da hankali ne ga auna nasarori ko akasin haka da aka cimma, game da ajandar inganta rayuwar nakasassu ta shekarar 2013 zuwa 2022.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China