Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da sauran bangarorin da abin ya shafa, don yin hadin gwiwa da nufin tabbatar da ganin an warware batun takaddamar nukiliyar ta ruwan sanyi ta hanyar tattaunawar sulhu.
Da yake mayar da martani, Trump ya ce Amurka ta yi matukar damuwa game da gwajin makaman nukiliyar da Koriya ta arewa ke aiwatarwa.
Trump ya ce Amurkar tana ganin kasar Sin a matsayin kasar dake da matukar muhimmanci bisa rawar da za ta iya takawa wajen warware takaddamar nukilyar, kuma Amurkar a shirye take ta ci gaba da tattaunawa, da kuma yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen lalibo bakin zaren warware wannan takaddama.
A yayin tattaunawar tasu ta wayar tarhon, shugaban na Sin ya bayyana cewa, a lokacin da shugaba Trump ya ziyarci kasar Sin a farkon wannan wata, shugabannin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi a tsakaninsu inda suka yi musayar ra'ayoyi game da muhimman batutuwa, kuma sun cimma matsaya mai muhimmanci kan batutuwa masu yawa, wadanda suke da matukar tasiri wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Xi ya bukaci bangarorin biyu da su cimma matsaya kan wadannan batutuwa, kana su yi kyakkyawan tsari na shirya musayar ra'ayoyi mai zurfi, don tabbatar da shirya zagaye na biyu na tattaunawa karkashin dukkan manyan matakan tattaunawar tabbatar da nasara tsakanin Sin da Amurka, kana su aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da ta muhimman ayyuka tsakanin kasashen biyu.
Trump ya amince da shugaba Xi dangane da nazartar nasarorin da ziyarar shugaba Trump ta haifar, da kuma tunanin da ake da shi na kara zurfafa matsayin dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Ahmad Fagam)