in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya ce samar wa Falasdinawa muhalli da ya dace zai tallafawa zaman lafiyar duniya
2017-11-30 09:56:16 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce samar wa al'ummar Falasdinawa muhallai cikakku da suka dace da bukatar su, zai tallafawa zaman lafiya da lumana a yankin da suke, da ma duniya baki daya.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, cikin sakon sa na taya murnar kewayowar ranar mara baya ga al'ummar Falasdinawa wadda MDD ke gudanarwa.

Xi ya ce, batun Falasdinawa, shi ne kashin bayan matsalar da ake fuskanta a Gabas ta Tsakiya, wadda kuma wajibi ne a magance ta, muddin ana fatan samun zaman lafiya da ci gaba tsakanin kasashen dake yankin na Gabas ta Tsakiya, ciki hadda su kan su al'ummar ta Falasdinu.

Ya ce, Sin na kan bakan ta, na ganin an wanzar da zaman lafiya tsakanin al'ummun Falasdinu da na Isra'ila. Don haka ne ma a cewar sa ta gabatar da wasu shawarwari 4 a watan Yulin da ya gabata, wadanda za su taimaka wajen cimma burin da ake da shi na ganin sassan biyu sun amince da juna, su kuma koma teburin shawarwari.

Shugaba Xi ya ce, a matsayin ta na wakiliyar dindindin a kwamitin tsaron MDD, kuma mai shiga a dama da ita tsakanin manyan kasashen duniya, Sin na fatan hada gwiwa da sauran kasashe, wajen ganin an gaggauta kaiwa ga wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China