Haka kuma, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana adawa da dukkan nau'ikan ta'addanci, tana kuma yin Allah wadai da harin da aka kai wa kasar, yana mai cewa, Sin za ta kuma goyi bayan kasar Masar wajen kiyaye zaman lafiya da yaki da 'yan ta'adda.
Haka zalika, Firaministan kasar Sin Li Keqiang, shi ma ya mika sakon jaje ga takwaransa na Masar Sherif Ismail, inda ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata.
Mr. Li ya ce, kasar Sin za ta hada hannu da kasar Masar wajen yaki da ta'addanci. (Maryam)