in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yammacin Afrika za su kaddamar da kasuwar makamashi ta shiyya
2017-11-30 11:18:40 cri
Masana a fannin samar da lantarki a yammacin Afrika suna gudanar da taro a kasar Ghana domin kammala tsara wani daftari daya kunshi yadda za'a kaddamar da kasuwar lantarki a shiyyar.

Mambobin kwamitin tuntuba da masu gudanar da harkokin lantarki a shiyyar yammacin Afrikar (ERERA), suna sake fasalin daftarin dokokin da suka shafi yadda za'a kafa da kuma tafiyar da al'amurran kasuwar makamashi ta shiyyar.

Kashin farko na kasuwar lantarki ta shiyyar, ana fata za ta shawo kan manyan matsaloli biyu da suka hada da na rashin samun damar amfani da lantarki da kuma tabbatar da tsaron lantarki a nahiyar, da farko dai an shirya kaddamar da shi ne a karshen shekarar 2016, amma daga bisani aka dage zuwa rubu'in farko na shekara mai zuwa.

Idan aka amince da kuma rattaba hannu kan dokokin, dukkan takardun dake kushe cikin daftarin za su kasance a matsayin muhimman abubuwa da za'a yi amfani da su wajen kaddamar da kashin farko na kasuwar makamashin a shekarar 2018.

Shugaban hukumar samar da lantarki na shiyyar Honore Bogler, ya bayyana cewa, idan aka samu nasarar kaddamar da kasuwar, hakan zai taimaka wajen inganata lantarki a kasashen yammacin Afrika, kuma zai taimaka wajen bunkasuwar harkokin ciniki a shiyyar.

Mahalarta taron sun yi amana cewa, samar da kasuwar lantarki a shiyyar zai yi matukar tasiri wajen daga matsayin ci gaban shiyyar yammacin Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China