in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Ana daukar matakai na zuba karin jari a fannin makamashi
2017-10-02 12:17:44 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin sa na kara yawan jari, da matakan warware matsalolin dake addabar fannin makamashin kasar.

Cikin jawabin sa na bikin cika shekaru 57 da samun 'yancin kan Najeriya da ya gabatar ta kafar talabijin mallakar kasar a jiya Lahadi, shugaba Buhari ya ce har yanzu makamashin lantarki na ci gaba da kasancewa babbar matsala ga ci gaban kasar, duk da cewa an kai ga samar da lantarkin da yawansa ya kai mega wat 7,001 ya zuwa ranar 12 ga watan Satumba. A cewar sa fatan gwamnatin kasar mai ci shi ne yawan lantarkin ya kai mega wat 10,000 nan da shekara ta 2020.

Kaza lika shugaban na Najeriya, ya bayyana sassan da gwamnatin sa ta fi baiwa muhimmanci, da suka hada da kara yawan makamashi ta hanyar amfani da karin fasahohi na hasken rana da na ruwa.

Ya kuma tabo batun sabon kudurin gwamnatin sa, na samar da guraben ayyukan yi a kalla 10,000, ga matasan kasar marasa ayyukan yi a jihohin kasar 36.

A fannin tattalin arziki kuwa, shugaba Buhari ta ce kasar sa ta samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki cikin watanni 7 a jere. A hannu guda kuma darajar kudin kasar Naira ya daga daga naira 525 kan ko wace dalar Amurka a watan Fabrairu, zuwa naira 360 kan ko wace dala a yanzu haka.

Ya ce gwamnatin sa na jagorantar tsare-tsare dake kara fitar da kasar daga matsin tattalin arziki da ta fuskanta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China