in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika za su cimma wa'adin kafa babbar kungiyar kasuwanci
2017-08-07 09:47:37 cri
Ana sa ran kasashen Afrika za su cimma wa'adin kafa kungiyar kasuwanci mafi girma a nahiyar nan da watan Oktoban 2017, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Sakatare janar na kungiyar kasuwancin ta gabashi da kudancin Afrika (COMESA), Sindiso Ngwenya, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, tuni kasashe 21 daga cikin kasashe 26 sun sanya hannu don amincewa da kafa kungiyar.

Ngwenya, ya ce, kafa gamayyar kungiyar ta kasuwanci marar shinge wadda ta kunshi kasashen gabashi da kudancin Afrika, kuma COMESA za ta tabbata kamar yadda aka tsara, kuma tun a ranar Lahadi COMESA ta isa kasar Kenya domin aikin sa ido kan zaben shugaban kasar wanda za'a gudanar a ranar 8 ga watan Augasta.

Ngwenya ya ce sauran kasashen 5 wadanda har yanzu ba su sanya hannu kan yarjejeniyar ba, an samu gagarumin ci gaba wajen cimma matsaya kan batun shigarsu kungiyar.

Bugu da kari, wasu kasashen Afrika biyu su ma sun nuna sha'awarsu na shiga kungiyar tattalin arzikin.

Ngwenya ya ce, zuwa karshen wannan shekara, kasashen Somaliya da Tunisiya su ma za su shiga cikin gamayyar kungiyar kasuwancin marar shinge.

Gamayyar kungiyar kasuwancin marar shinge ta kunshi kasashe 28, ta hade yankuna masu girman murabba'in kilomita miliyan 18.3, wanda ya kai adadin kashi 61 cikin 100 na yawan al'ummar nahiyar Afrika baki daya. (Ahamda Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China