in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Garambawul ga shirin hakar ma'adinai a Ghana zai bunkasa ci gaban tattalin arziki
2017-08-26 12:54:32 cri

Kasar Ghana na sa ran shirin yi wa harkokin hakar ma'adinai garambawul zai mai da bangaren jigo wajen habakar tattalin arzikin kasar.

Shugaban shirin garambawul din da ya kunshi dabaru da dama Isaac Karikari, ya ce hakar ma'adinai za ta inganta rayuwar al'ummomin dake da albarkatu tare da kawar da matsalar amfani da yara wajen hakar ma'adinai.

Da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin jiya Jumma'a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na yini biyu kan fatan Afrika game da hakar ma'adinai, Isaac Kikari ya yi bayanin cewa, samar da guraben aikin yi musammam a wuraren da ake hakar ma'adinai, zai zama muhimmiyar moriyar da Ghana za ta samu daga aiwatar da aikin.

Kashi 20 cikin 100 na kudin aikin da ake sa ran zai lakume dala miliyan 200 zai fito ne daga gwamnatin Ghana, yayin da hukumomin raya kasashe za su bada kashin 50, inda kuma sauran za su fito da kamfanonin hadin gwiwa masu zaman kansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China