Da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, Mr. Kale ya ce ko da yake an samu ci gaba, amma hakan bai sauya yanayin da al'ummar kasar ke ciki ba.
Ya ce Najeriya na da matakai daban daban da za ta dauka, kafin kaiwa ga matsayin da kowa zai gani a kar. Babban dalilin da ya sanya kuwa har yanzu talakawan kasar ba su fara gani a masakin su a cewar jami'in, shi ne dogaron da kasar ke yi mafi yawa, daga kudaden da ake samu daga cinikayyar danyen mai.
A ranar Talata ne dai hukumar kididdigar ta Najeriya, ta bayyana cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arziki da ta dage bata fuskanci irin sa ba, bayan da GDPn kasar ya karu da kaso 0.55 bisa dari, a rubu'i na biyu na shekarar nan da muke ciki.
Tun a rubu'i na biyu na shekarar bara ne kasar ta dulmiya cikin halin komadar tattalin arziki, matakin da ya haifar da karin matsin rayuwa ga al'ummar kasar. (Saminu)