in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Kasashen Kenya da Habasha na iya shan gaban Najeriya da Afirka ta Kudu wajen janyo masu zuba jari
2017-09-15 10:22:18 cri
A jiya ne wata kungiyar tuntuba da ta kware a fannonin siyasa da tsaro ta kasa da kasa, ta fitar da wani rahoto dake nuna cewa, nan ba da dadewa ba kasashen Kenya da Habasha za su sha gaban manyan kasashen nahiyar a fannin tattalin arziki wato Najeriya da Afirka ta kudu da Masar wajen gasar masu sha'awar zuba jari.

Rahoton wanda aka fitar a birnin Johannesburg na kasar Afitka ta kudu, ya kuma nuna cewa, yayin da kasashen Najeriya da Afirka ta kudu suke farfadowa daga komadar tattalin arziki da suka tsunduma, har yanzu suna fuskatar wasu hadurra. A hannu guda ita kuma kasar Habasha, daya daga cikin kasashen nahiyar da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa, ta dara dukkan kasashen nahiyar, kamar yadda binciken ya nuna.

Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2016 da ta gabata, kasar ta Habasha ta janyo jari kai tsaye daga waje da ya kai dala miliyan 3.2. Kana daga shekarar 2010 zuwa 2015 matsakaicin ci gaban tattalin arzikin kasar ya kai kaso 10 cikin 100,da kuma kaso 6.6 cikin 100 a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya ce kasar Kenya ta samu matsakaicin ci gaban tattalin arzikin da ya kai kaso 6 cikin 100 a wadannan shekaru da muka ambata a baya, ana kuma saran ci gaban ya kai kaso 5.4 cikin 100 a wannan shekara.

Daga karshe rahoton ya yi nuni cewa, bangaren makamashin Najeriya, ya taimakawa kasar. Koda ya ke rahoton ya ce, hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a yankin Niger Delta da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, suna daga cikin dalilan da suka sanya koma bayan tattalin arzikin kasar daga kaso 6.3 cikin 100 a shekarar 2014, zuwa kaso 2.7 cikin 100 a shekarar 2015.

Najeriya dai ta samu ci gaban tattalin arziki na kaso 1.6 cikin 100, kuma ana saran ci gaban ya kai kaso 1.1 a wannan shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China