A yayin taron, ba a zartas da daftarorin da bangarorin biyu suka gabatar ba. Lamarin da ya nuna cewa, kwamitin binciken zai kammala aikinsa a yau 17 ga wata, kamar yadda aka tsara tun farko.
Kasashen Amurka da Rasha dai sun bukaci a tsawaita wa'adin aikin gudanar da binciken wannan zargi zuwa shekara daya. Amma a cikin daftarin da kasar Rasha ta gabatar, ta zargi hanyar yin bincike da kwamitin gudanar da wannan bincike yake bi, sa'an nan ta nemi a tattara da kuma yin nazari kan bayanai game da yadda wadanda ba na gwamnati ba suka taba yin amfani da makamai masu guba. A sa'i daya kuma, cikin daftarin da kasar Amurka ta gabatar da shi, ta bukaci a tsawaita wa'adin aikin zuwa watanni 12, a maimakon watanni 24 wato kamar yadda ta bukata tun farko. (Maryam)