in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kori wasu ministoci a Morocco bisa jinkirta gudanar da ayyukan raya kasa
2017-10-25 09:23:25 cri
Sarkin Morocco Mohammed na VI, ya kori wasu ministocinsa 4, saboda hannu da suke da shi wajen jinkirta aiwatar da wasu ayyukan raya kasa a birnin Al Hoceima dake arewa maso gabashin kasar.

Ministocin da aka kora sun hada da na ilimi da na lafiya da na tsara kasa da sakataren gwamnatin mai kula da horo kan sana'o'in hannu.

A cewar kwamitin bincike da sarkin ya kafa a watan Yunin da ya gabata, galibin ayyukan babban shirin raya kasa na "Lighthouse of the Mediterranean" da aka kaddamar a birnin Al Hoceima a shekarar 2015, sun gamu da cikas saboda jinkiri ko gazawa wajen aiwatar da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China