Taron na 2017 zai samu halartar sama da wakilai 400 daga kasashen Afrika 45 domin tattauna batun hadin kan kasashen Afrika game da yaki da ta'addanci, da tsattsauran ra'ayi da aikata laifuka a kan iyakoki.
Shugaban dandalin Driss Benamer ya yi wa taron manema labarai karin haske game da manufar shirya taron. Ya ce taron zai mai da hankali ne kan manyan batutuwa 3 da suka hada da batun ta'addanci da yin kutse ta hanyar na'urorin zamani, da batun sabbin hanyoyin masu tsattsauran ra'ayi, da sabbin kalubalolin bakin haure da masu aikata laifuka a kan iyakokin kasashe da kuma duba batun hadin kai tsakanin kasashen Afrika da irin sabbin kalubalolin dake tattare da batun.(Ahmad Fagam)