in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tusa keyar bakin haure 25 daga Libya zuwa Nijer
2017-11-13 09:27:31 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Libya ya sanar da cewa, kimanin bakin haure 25 'yan jamhuriyar Nijer da suka hada da mata da yara aka kwashe daga birnin Tripoli na kasar Libya, inda aka mayar da su Nijer a ranar Asabar.

Shirin MDD ya bayyana cewa, a halin yanzu 'yan tawagar suna kan hanyarsu ta zuwa Nijer a matsayin wani bangare na shirin kwashe jama'a na hadin gwiwa tsakanin hukumar ba da agaji ta MDD UNHCR, da gwamnatin Libya, da kuma gwamnatin jamhuriyar Nijer. Daga cikin bakin hauren 25, akwai mata 15, da maza 6, sai kananan yara 4.

Shirin ya nanata muhimmancin kwashe jama'ar a matsayin wani mataki na kiyaye rayuwar 'yan gudun hijira marasa galihu dake Libya wadanda aka tilasta musu yin tafiya mai cike da hadari ta cikin teku, domin neman mafaka a kasashen ketare.

Sakamakon tashin hankali da tabarbarewar tsaro da ya barke a shekarar 2011, Libya ta kasance wata matattara da bakin haure ke amfani da ita wajen tsallakawa kasashen Turai ta cikin tekun Mediterranean.

Bakin hauren da sojin ruwan Libya suka ceto, ana tsare su ne a wata cibiya inda suke rayuwa cikin yanayin matsin rayuwa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China