in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD ya gana da firaiministan Libya game da warware rikicin kasar ta hanyar siyasa
2017-11-13 09:54:16 cri
Wakilin musamman na sakatare janar na MDD, kuma shugaban shirin kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Libya Ghassan Salame, ya gana da firaiministan kasar Libya wanda ke samun goyon bayan MDD Fayez Serraj, a birnin Tripoli domin tattaunawa game da matakan siyasa da za a yi amfani da su wajen warware rikicin kasar.

A wata sanarwa daga ofishin yada labarai na firaiministan, tattaunawar da suka gudanar ta mayar da hankali ne game da irin ci gaban da aka samu na baya bayan nan wajen warware rikicin siyasar kasar da kuma matakai na gaba da za'a bi wanda Salame ya gabatar da su, wanda ake sa ran zai shafi batun zaben shugaban kasar da na majalisar dokokin kasar.

Salame zai gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaron MDD game da irin nasarorin da aka samu na warware rikicin siyasar kasar Libya a ranar 16 ga watan nan.

Haka zalika, Salame ya gana da jakadan Italiya a kasar Libya Guiseppe Perrone, a Tripoli a ranar Lahadi, kuma za su tattauna game da irin goyon bayan da Italiya ke baiwa MDD da kuma batun taron kwamitin tsaron MDD da za'a gudanar a nan gaba game da batun na Libya.

Wakilin MDD ya kuma gana da jakadan Turkiyya a kasar Libya Ahmad Dogan, kuma ya jaddada goyon bayansa ga gwamnati da al'ummar Turkiyya sakamakon garkuwar da aka yi da wasu ma'aikatan 'yan asalin kasar Turkiyyar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China