Da take jawabi a wajen bikin ranar matasa ta duniya a babban birnin siyasa na Dodoma, jami'ar Hukumar UNFPA Hashina Begum, ta ce ciki da 'yan mata ke yi da karancin shekaru, shi ne babban tarnaki da ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.
Ta ce sun kuduri niyyar ci gaba da hada hannu da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen magance abubuwan dake haddasa matsalar a Tanzania.
Hukumar kididdiga ta kasar ta ce kimanin kashi 21 na 'yan mata a Tazania dake tsakanin shekaru 15 zuwa 19 sun taba haihuwa.
Hasina Begum ta ce za a iya magance matsalar ta hanyar koyar da matasa ilimin da ya shafi hanyoyin daukar ciki tare da samar musu da ingantaccen tsarin kiwon lafiya.
Ta ce yin ciki da karancin shekaru shi ne babban kalubale da ke kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a galibin kasashen Afrika, ciki har da Tanzania.
Jami'ar ta ce ya kamata gwamnatin Tanzania ta mayar da hankali sosai wajen yaki da matsalar. (Fa'iza Mustapha)