Kasar Sin na ci gaba da karfafa aikin nazari kan kudin internet, ganin cewar kasar na fatan yin amfani da sabbin fasahohin zamani domin sanya kudin takarda kan internet, da kuma saukaka hada hadar kudi cikin adalci da inganci.
Tun lokacin kasar Sin ta kaddamar da shirye shirye domin kudin fasahar zamani bisa tsarin doka a shekarar 2014, an gabatar da shirin a zagaye biyu na sake dubawa a yayin da ake gudanar da wani bincike mafi zurfi, in ji Yao Qian, wani jami'in babban bankin tsakiyar kasar dake jagorantar cibiyar bincike kan kudin fasahar zamani.
Da farko, Sin za ta shigar kudin a cikin wasu kasuwannin hada hadar kudi, tare da bunkasa yin amfani da su sannu a hankali da taka tsantsan, in ji mista Yao Qian, ba tare ba da wani cikakken jadawali ba.
Idan aka kwatanta da kudin takarda da aka saba amfani da shi, kudin fasahar zamani na amfani da fasahohin tantancewa na zamani, da kuma sauki sosai wajen hada hada, da kyautata ingancin hada hada da ingiza adalci.
Bitcoin, shi ne kudin fasahar zamani da aka fi yin amfani da shi, wanda kuma ba ya da wata alaka da wani banki ko gwamnati, na baiwa masu sayayya damar kashe kudi a asirce. (Maman Ada)