in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya tattauna da shugaban kasar Panama
2017-11-18 13:42:42 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna a jiya Juma'a da takwaransa na kasar Panama Juan Carlos Varela Rodríguez dake ziyara a kasar Sin, a babban dakin jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing.

Yayin tattaunawar, Xi Jinping ya ce shugaba Juan Carlos, shi ne shugaban kasar Panama na farko da ya kawo ziyara kasar Sin, kana, shugaban wata kasa dake nahiyar Latin Amurka na farko dake ziyara a kasar tun bayan kammala babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 19, inda ya ce ya na masa maraba da zuwa a madadin jama'ar kasar Sin.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta sanya nahiyar Latin Amurka a wani muhimmin bangare yayin da ake aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", ya na mai cewa kasar Panama muhimmiyar kasa ce cikin "hanyar siliki na teku a karni na 21" a Latin Amurka.

Ya ce kamata ya yi, bangarorin biyu su bi shawarar "ziri daya da hanya daya", ta yadda za su mai da hadin gwiwarsu kan muhimman bangarori da za su amfane su.

A nasa bangare, shugaba Juan Carlos Varela ya bayyana cewa, Panama ta na son yin kokari tare da kasar Sin, wajen kara mu'amala tsakanin shugabannin kasashen biyu, da sada zumunta a tsakanin jama'arsu, da kara yin hadin gwiwa a fannonin ciniki da zuba jari da hada-hadar kudi da zaman rayuwar jama'a da yaki da talauci da ayyukan more rayuwa da sauransu.

Har ila yau, ya ce Panama ta na goyon bayan shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya gabatar, inda ya ce kasar za ta shiga aikin raya hanyar siliki na teku, da samar da gudummawa wajen aiwatar da shawarar a Latin Amurka, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China