in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Djibouti sun amince da karfafa hadin gwiwa mai ma'ana
2017-11-23 21:13:08 cri
Kasashen Sin da Djibouti, sun amince da kafa wani salon hadin gwiwa da zai amfani sassan biyu, a wani mataki na karfafa alakar su daga dukkanin fannoni.

Sanarwa hakan dai ta biyo bayan ganawar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi da takwaransa na Djibouti Ismail Omar Guelleh a dakin taron jama'a na kasar Sin dake nan birnin Beijing a yau Alhamis.

Shugaba Guelleh, shi ne shugaban kasa daga nahiyar Afirka na farko da ya ziyarci kasar Sin, tun bayan kammala taro na 19 na wakilan JKS da ya gabata a watan Oktoba.

Mahukuntan kasar Sin dai sun yi maraba da shigar Djibouti shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya", wadda karkashinta, tuni sassan biyu suka fara hadin gwiwar samar da muhimman ababen more rayuwa, ciki hadda ginin layukan dogo, da tashar jiragen ruwa, da samar da ruwan sha mai tsafta. Sauran fannonin sun kunshi na shimfida bututun iskar gas, da gina yankin ciniki cikin 'yanci da kuma hadin gwiwa a fannin raya noma.

Shugaba Guelleh na ziyarar aiki ne a nan kasar Sin tsakanin ranekun Laraba zuwa Jumma'a. Ya kuma bayyana aniyar kasarsa, ta shiga a dama da ita a wannan shawara ta "ziri daya da hanya daya", tare da bunkasa hadin gwiwa da kasar Sin, a fannin samar da ababen more rayuwa da sauran sassa na inganta rayuwar al'umma. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China