Yayin tattaunawar tasu, Sarki Salman ya taya Xi Jinping murnar sake zama babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar karo na 19 cikin nasara, inda ya kuma ya jaddada cewa, babu tantama babban taron zai jagoranci al'ummar kasar Sin wajen samun nasara.
Salman ya kuma ce, alakar dake tsakanin Saudiyya da Sin na samun babban ci gaba, kuma kasarsa na fatan fadada hadin-gwiwa tare da Sin, musamman ma a fannonin da suka shafi makamashi, da harkokin kudi. Kaza lika Saudiyya na fatan zama babbar aminiyar kasar Sin a yankin Gulf, da dukufa ka'in da na'in, kan zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da kasar Sin, al'amarin da zai taimaka ga tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.
A nasa bangaren kuma, shugaba Xi Jinping ya ce, Sin da Saudiyya aminan juna ne, wadanda ke kara samun amincewa da hadin-gwiwa tsakaninsu. Har ila yau kasar Sin na fatan ci gaba da kokari tare da Saudiyya, domin kara aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', da habaka hadin-gwiwa daga fannoni daban-daban. (Murtala Zhang)