in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe ya yi jawabi ba tare da bayyana batun murabus ba
2017-11-20 11:33:17 cri
Jiya da dare ne, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi jawabi ta kafar telebijin a fadar shugaban kasar, sai dai bai bayyana batun yin murabus ba. Yana mai cewa zai shugabanci babban taron wakilan jam'iyyar dake jan karagar mulkin kasar a wata mai zuwa.

Kafin wannan, jam'iyyar ZANU-PF ta gudanar da taron kwamitin kolin na jam'iyyar na musamman, inda aka kori Mugabe daga shugabancin jam'iyyar kana babban sakataren jam'iyyar. Kana aka tsaida kudurin mayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa a matsayin memban jam'iyyar aka kuma nada shi a matsayin shugaban jam'iyyar kuma babban sakatarenta.

A jawabinsa, Mugabe ya ce, bai amince da kudurorin da jam'iyyar ta tsaida a wannan rana ba.

Ya ce, ya kamata a canja mukamin shugaban jam'iyyar bisa oda. Ana fatan warware matsalar a yayin taron wakilan jam'iyyar ZANU-PF da zai shugabanta a watan Disamba mai zuwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China