in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Rasha sun kaddamar da hari ta sama kan IS a Syria
2017-11-05 13:57:26 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar cewa a ranar Asabar darakun sojin kasar Rashar suka harba wasu boma bomai ta sama kan wasu kayayyakin mayakan 'yan ta'adda na IS a gabashin kasar Syria.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron ta fitar tace, wuraren da sojojin suka yi niyyar kai harin sun hada da wajen da 'yan ta'addan suke adana makamai da harsasansu da wasu wuraren taruwar 'ya'yan kungiyar IS, kuma dukkan wuraren suna kusa da birnin Abu Kamal ne dake gabashin lardin Deir ez-Zor a Syria kusa da kan iyakar kasar Syrian da Iraqi.

Sanarwar tace, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa, an yi nasarar lalata dukkan wuraren da ake son kaddamar da hare haren, kuma dukkan jiragen saman yakin da aka yi amfani dasu wajen gudanar da akin sun koma sansaninsu dake kasar Rasha bayan kammala aikin.

A yan kwanakin nan, dakarun sojin kasar Rasha sun kara azama a kokarin da suke yi na murkushe 'yan ta'adda na IS a Syria. Ma'aikatar tsaron Rashar ta ayyana cewa kimanin hare hare ta sama 18 ta kaddamar kan maboyar dakaraun na IS daga ranar Larabar data gabata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China