Rahotanni na cewa, an kai harin ne a wata tashar binciken ababan hawa dake arewacin birnin Deir ez-Zor, wadda karkashin ikon sojojin Syria dake karkashin jagorancin dakarun yankin Kurdawa.
Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya bayar da labari cewa, an kai wani harin bam a sansanin 'yan gudun hijira, inda maharin ya kutsa da mota shake da bama-bamai cikin sansanin 'yan gudun hijirar, harin ya kuma haddasa mutuwa da raunatar mutane da dama ciki har da mata da yara.
Kungiyar dake binciken batun kare hakkin dan Adam ta kasar Syria mai cibiya a birnin London na kasar Birtaniya ta bayyana cewa, kungiyar IS ce ta kai wannan hari.
A jiya ne, sojojin gwamnatin kasar Syria suka shiga birnin Deir ez-Zor, inda suka kwace birnin daga hannun mayakan IS, bayan da suka shafe shekaru 3 suna rike da birnin. Bangaren soja na kasar Syria ya sanar a ranar 3 ga wannan wata cewa, yanzu birnin Deir ez-Zor ya fita daga hannun kungiyar IS. (Zainab)