Kiran ya zo ne bayan sojoji sun karbe ragamar Gwamnatin kasar a farkon makon nan.
Lardunan, ciki har da mahaifarsa ta Mashonaland ta yamma, na zargin Mugabe da kyale kafuwar wani tsagi cikin jam'iyyar, suna masu kira da a rushe tsagin G40 da suke zargin uwar gidansa Grace Mugabe na jagoranta.
Cikin rahoton da suka fitar, lardunan sun bukaci a mayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa mukaminsa cikin jam'iyyar da kuma Gwamnati.
Sun kuma ba kwamitin tsakiya na jam'iyyar shawarar gudanar da taro na musammam cikin sa'o'i48 domin sake daidaita jam'iyyar ta yadda za ta dace da yanayin da ake ciki a yanzu.
A nata bangaren, Kungiyar tsoffin 'yan gwagwarmaya da suka yi yakin neman 'yancin kasar, ta yi kira ga al'ummar kasar su yi fitar dango don halartar wani gangami a yau Asabar a birnin Harare, domin mara baya ga matakin da sojojin kasar suka dauka.
Rundunar sojin dai ta ce tana tautaunawa da Mugabe domin daukar mataki na gaba. (Fa'iza Msutapha)