in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar Zimbabwe sun bukaci shugaba Mugabe da ya yi murabus
2017-11-19 13:41:06 cri
Jiya Asabar da safe, al'ummomin kasar Zimbabwe da dama sun taru a titunan birnin Harare, fadar mulkin kasar, inda suka yi zanga-zanga domin nuna goyon baya ga rundunar sojan kasar, da kuma matakan sojan da ta dauka, haka kuma, sun yi kira ga shugaban kasar Robert Gabriel Mugabe da ya yi murabus ba tare da bata lokaci ba.

Akwai 'yan jaridun da suka bayyana cewa, da misalin karfe 10 da safe, galibin manyan tituna dake cikin cibiyar birnin Harare suna cike da mutanen dake yin zanga-zanga, inda suka tashi zuwa fadar shugaban kasar, kana sun yi kira ga shugaba Mugabe da ya yi murabus, sun kuma nuna goyon bayansu ga rundunar sojojin kare kasar.

Haka kuma, akwai mutane da dama da suka taru a gaban kofar fadar shugaban kasar, wasu kuma sun yi yunkurin shiga cikin fadar, sai dai jami'an tsaro sun hana su shiga fadar shugaban kasar.

Ya zuwa ranar 18 ga wata, zanga-zangar ya bata yanayin sufuri a birnin Harare, amma bai haddasa rikici mai tsanani a birnin ba, kuma an kawo karshen zanga-zanga da yammacin wannan rana.

Bisa labarin da aka samu daga kafofin watsa labarai na kasar, an ce, hukumomin larduna 10 na kasar dake karkashin jagorancin jam'iyyar mai mulki ta kasar Zimbabwe watau jam'iyyar ZANU-PF sun fidda sanarwa cewa, an bukaci shugaban kasar Robert Gabriel Mugabe da ya yi murabus. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China