in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A shirya SADC take ta taimakawa Zimbabwe
2017-11-18 13:28:11 cri
Shugaban kungiyar raya yankin kudancin Afrika SADC Jacob Zuma, ya ce a shirye kungiyar take, ta bada dukkan taimako da ake bukata ga al'ummar Zimbabwe domin warware takkadamar siyasar kasar.

Jacob Zuma, wanda kuma shi ne shugaban kasar Afrika ta Kudu wadda mamba ce ta kungiyar, ya bayyana a Gaborone babban birnin Botswana cewa, kungiyar SADC ta damu ainun da al'amuran dake faruwa a Zimbabawe, inda ya ce ta na fatan cewa, ba za su kai ga sabawa kundin tsarin mulkin kasar wajen sauya Gwamnati ba.

Shugaba Zuma ya bayyana haka ne gabanin jawabinsa ga taro karo na 4 tsakanin Botswana da Afrika ta kudu. Inda ya ja hankalin dukkan bangarori da takkadamar ta shafa, da su tabbatar da ba a kaucewa tsarin zaman lafiya da tsaro da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada ba.

Da yake mai da martani ga Shugaba Zuma, Shugaban Botswana Seretse Khama Ian Khama, ya ce ya na da tabbacin za su samarwa al'ummar Zimbabawe mafita, inda ya yi alkawarin zai ci gaba da tuntubar Shugaba Zuma don tattauna al'amarin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China